Donald Trump Ya Yi Aikin Alkairi Ga Addinin Musulunci
Daga S-bin Abdallah Sokoto.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya baiwa jami'an tsoron kasar sa umurnin su hanawa Kamfanin kasar Chana shigowa da kaya cikin kasar sa ta Amurka, Saboda muzgunawar da gwamnatin Chana ke yiwa musulmi yan kabilar Uighur.
A cewar Donald Trump sun dauki wannan tsatstsauran mataki ne saboda ana tursasa wa musulmin yin aikin dole a wadannan ma'aikatu tamkar 'yan gidan yari, wanda hakan sam bai dace ba, kuma baza mu lamunta da wannan ba.
Allah sarki duniya, a lokacin da Donald Trump yana neman shugabancin kasar Amurka mafi yawancin musulman duniya kallonsa mu ke a matsayin wanda idan ya ci zabe zai takurawa musulman duniya, zai hanawa musulmai walwala a kasar Amurka.
Amman cikin ikon Allah a tarihin shugabannin kasar Amurka ba taba shugaban da ya baiwa al'ummar musulmi damar gudanarda sha'aninsu irin Donald Trump ba, dudda kasancewar a farkofarkon mulkinsa wasun mu mun masa kallon mutun mai tsananin kiyayya da addinin musulunci.
Hakazika, dudda ana masa kallon dan tada-zauna-tsaye har kawo yanzu ba mu ji kasar Amurka na yaki da wata kasa ta musulmi a zamanin mulkinsa ba, sabanin zaman mulkin Judge Bush da Barack Obama, wadanda ko shakkka babu sun cutarda duniyar musulunci.
Yanzu haka al'ummar kasar na kokarin ganin sun kada shi a zaben da a yi nan gaba, saboda bai kasance mutun mai yaki da kasashen duniya ba. Saboda dama su ta wannan hanya ne su ke samun arziki a kasar su da walwalar da su ke samu.
Kuma da wannan mu ke rokon Allah ya bashi nasara a zaben da yake tafe.
No comments:
Post a Comment